Sweden

Masu fafutukar sanya hijabi a Sweden sun kai kukansu gaban Ministar Shari’a

Wasu mata Musulami sanye da hijabi a kasar Faransa
Wasu mata Musulami sanye da hijabi a kasar Faransa Reuters/AFP

Ministar ma’aikatar shari’a a kasar Sweden Beatrice Ask, ta gana da wata tawaga ta masu fafutukar ganin an bai wa mata damar sanya hijibi a kasar. Ganawar dai ta zo ne kwanaki kadan bayan an kai wa wata mata mai dauke da juna biyu hari, saboda ta sanya hijabi a kasar. 

Talla

Foujan Rouzbeh Shugabar kungiyar da ke fafutukar ganin an bai wa mata damar sanya hijabi a kasar wadda ke cikin wannan tawaga da ta gana da minsitar, ta ce a lokacin ganawar sun tattauna ne dangane da yadda ake nunawa masu sanya hijabi kyama a cikin kasar.

Kokarin kafa wannan kungiya ta fafufuka da kuma ganawa da hukumomin kasar da matan suka yi, ya biyo bayan harin da aka kai wa wata mata a wata unuguwar da ke wajen birnin Stockholm a daidai lokacin da take shirin shiga motarta a ranar juma’a, kuma bayanai sun tabbatar da cewa an kai harin ne saboda matar tana sanye ne da hijabi.
Tuni dai wannan matar wadda ‘yar kasar ta Sweden ce ta shigar da kara a gaban kotu dangane da wannan hari da aka kai mata, inda wasu bayanai ke cewa maharan sun furta kalaman nuna kyamar baki da kuma mabiya addinin musulmi, sannan kuma suka ambaci sunan hijabi kamin su kai mata hari.

Ita dai ministar shari’a Biatrice Ask ta ce gwamnatin kasar na iya kokarinta domin fada da wannan matsala, kuma batun nuna kyamar baki ko kuma wariyar jinsi, matsala ce da kasar ke fada da ita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.