Faransa

Zanga-zangar a kasar Faransa

Masu zanga-zangar a kasar Faransa.
Masu zanga-zangar a kasar Faransa. REUTERS/Charles Platiau

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar a jiya talata a kasar Faransa domin nuna rashin amincewar su da tsarin biyan kudin fansho a kasar.An dai gudanar da wannan zanga-zanga ne a sassa daban –daban na kasar.  

Talla

Sanadiyar yi wa tsarin biyan kudin fansho kwaskwarima ya janyo cece kuce a shekarar 1995 da kuma 2010 hakkan an haifar da zanga zanga da kuma yaje yajen aiki sai dai bayan da ta yi nata sauye sauye a game da wannan doka, gwamnatin masu ra’ayin gurguzu ta kasar da farko ba ta hadu da fushin al’umar kasar sosai ba sai a wannan karo.

Kungiyoyin hudu ne a kasar suka yi kira a jiya talata na yin zanga-zanga a sassa daban daban na kasar amman sai dai wasu daga cikin kungiyoyin sun bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi wa dokar gyra.

Akalla ma’aikata dubu dari uku da sittin ne cikin su har da matasa da kuma wadanda suka yi ritaya suka shiga zanga zanga yayin da ‘yan sanda suka ce yawan masu zanga zangar bai wuce dubu dari da hamsin da biyar a yankuna 170 na kasar ba.

A ranar 18 ga watan satumba mai zuwa Faransa za ta fitar da sabon tsarin biyan fanshon da aka yi gyaran fuska sanadiyar matsin lambar daga kungiyar Tarrayar Turai ke yi wa kasar, kuma hakkan zai bai Faransa damar samun rarar kudaden da yawansu zai kai Euro biliyan 20 kafin shekara ta 2020

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.