Geogia

Yau ake zaben shugaban kasar Geogia

Shugaban Geogia mai barin gado, Mikheil Saakachvili da madugun 'yan adawa, Bidzina Ivanishvili
Shugaban Geogia mai barin gado, Mikheil Saakachvili da madugun 'yan adawa, Bidzina Ivanishvili vesti.az

A yau lahadi, al’ummar kasar Geogia ke gudanar da zaben shugaban karo, karo na 4 kenan tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta daga tsohuwar tarayyar Soviett a shekarar 1991. A wannan karo dai shugaban kasar Mikheil Saakachvili da ake kallo a matsayin mai ra’ayin kasashen Yamma, ba zai tsaya takara ba, to sai dai duk haka ana ganin cewa rawar da zai taka na iya yin tasiri a game da wanda zai sami nasara a wannan zaben.