Birtaniya

Birtaniya za ta soke shirinta na biyan kudade wajen neman bizar shiga kasar

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Stefan Wermuth

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta soke shirin ta na sanya ‘yan wasu kasashen Asiya da Afrika biyan Dala 4,800 wajen neman bizar zuwa kasar.

Talla

Gwamnatin kasar ta dauki aniyar haka ne dan ganin ta hana jama’ar kasashen India, Pakistan, Sri Lanka, Ghana da Nigeria, da take ganin kasashensu a matsayin masu hadari, sun daina wuce lokacin da ake basu na zama a kasar.

Tuni shirin sanya kudin ya gamu da suka, inda ministan harkokin wajen Nigeria da aka sauke, Olugbenga Ashiru ya bayyana matakin a matsayin abinda ya saba kudirin kasashe renon Ingila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.