Girka

An yi arangama da ‘yan sandan Girka da masu zanga zanga

Masu bore da 'yan sanda a Girka
Masu bore da 'yan sanda a Girka rfi

Aranggama tsakanin ‘yan sanda da ‘yan majalisun na bangaren adawa ta barke a Girka bisa dalilin rufe gidan watsa labarai na ERT da aka kulle tun a watan Yulin da ya gabata.

Talla

‘Yan sandan da suke gadin gidan watsa labaran dake Arewacin birnin Athens sun fuskanci turjiya daga ‘yan adawan na jam’iyar Syriza.

Rufe gidan watsa labaran ya samu suka matuka daga jama’ar kasar a daidai lokacin da ake shirin kada kuri’a amincewa ko kuma akasain haka da gwamnatin kasar.

A yammacin yau lahadi ake sa ran majalisar dokokin kasar za ta kada kuri’ar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.