Italiya

An Cafke mutane 16 da ake zargi suna safarar mutane a Italiya

Yankin Sicily dake Kasar Italiya da ake shigar da mutane cikin nahiyar turai
Yankin Sicily dake Kasar Italiya da ake shigar da mutane cikin nahiyar turai Nasa

Sojojin ruwan kasar Italiya sun kama wasu mutane 16 da ake zargin cewar masu safarar mutane ne, a kusa da gabar ruwan Libya. Hukumomin kasar sun ce, sun kama mutanen ne bayan sun dade suna bin sawun su, sakamakon bayanan asirin da suka samu. Sojojin sun ceto wasu bakin haure 176 'Yan kasar Syria a cikin wani kwale kwale da ke kan hanyar zuwa Turai.

Talla

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.