Fransa

'Yansandan Faransa sun kaddamar da samame kan masu fataucin makamai

Makamai
Makamai © AFP/Anne-Christine Poujoulat

Hukumomin kasar Faransa sun cafke mutane 45 a wani samame da suka kaddamar da nufin kama masu fataucin makamai zuwa sauran sassa na duniya.

Talla

A wata sanarwa da suka fitar a yau, hukumomin ‘yan sandar kasar sun ce babbar manufar kaddamar da wannan samame ita ce kwace dimbin makamai da kuma albarusai da ake fataucinsu daga yankin Balkan da kuma Slovakia tun daga shekara ta 2009, sannan kuma ake ratsawa da su a gabar ruwan kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI