Birtaniya

Ana tuna harin Lockerbie a Birtaniya

Kaburburan wadanda suka mutu a harin Lockerbie kasar Scotland
Kaburburan wadanda suka mutu a harin Lockerbie kasar Scotland Reuters/David Moir

A rana irin ta yau ce wani jirgin sama ya tarwatse a garin Lockerbie da ke yankin Scotland shekaru 25 da suka gabata inda Fasinjan jirgin 259 suka mutu da wasu mutane 11 a kasa. Akwai addu’oi da ‘Yan uwan mamatan za su gudanar a Birtaniya da Amurka.

Talla

A ranar 21 ga watan Disemba ne aka kai harin a shekarar 1988, kuma Dan kasar Libya Abdelbaset Ali Mohmet al-Megrahi shi ne mutum guda da aka kama da laifin kai harin kafin ya mutu a bara.

A cikin harin na Lockerbie akwai mambobin Jami’ar Syracuse wadanda suka mutu su 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.