Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha za ta farfado da dangantakar tsohuwar Daular Soviet

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ©Reuters.
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace suna dab da kaddamar da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Rasha da Belarus da Kazakhstan domin farfado da dangantar da ke tsakaninsu a tsohuwar Daular Soviet. Wannan yunkurin kuma na zuwa ne bayan Rasha ta cika wani alkawali na tallafawa kasar Ukraine domin ceto tattalin arzikinta.

Talla

Wannan wani yunkuri ne na Rasha domin kafa kungiya ta kawancen kasuwanci da tsoffin kasashen Daular Soviet, Belarus da Kazakhstan don adawa da Kungiyar Tarayyar Turai.

Shugaban Rasha Vladimir Putin yace akwai wata ganawa da zasu yi tsakanin shi da shugaban Kazakhstan Nursultan Nazarbayev da shugaban Belarus Alexander Lukashenko domin tattauna batun kafa kungiyarsu da zasu kaddamar a 2015.

Tuni wakilan Russia da Kazakhstan da Belarus suka zana wani daftari game da yadda dokokin kawancen nasu zai kasance.

Mista Putin ya bayyana fatar Ukraine zata shigo cikinsu, musamman fahimtar juna da ke tsakanin shi da Viktor Yanukovych.

A baya dai Rasha ta razana Ukraine da barazanar takumkumi idan har ta kulla kwancen kasuwanci da Turai, wanda ya sa dole Ukraine ta koma ma Rasha, lamarin da ya haifar da bore daga ‘Yan adawa a Ukraine masu ra’ayin Turai.

Rasha tana neman bullo da wata hanya ce ta inganta karfin fada aji a duniya idan har ta samu nasarar hada kawancen kasuwaci da tsoffin kasashen Daular Soviet, inda yanzu haka Rasha ke janyo hankalin Armenia da Kyrgyzstan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.