Faransa

Ministan tsaron Faransa ya kai ziyara Mali

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Laurent Dubrule

A yau Ministan Tsaron kasar Faransa, Jean – Yves Le Drian ya fara wata ziyara a birnin Gao dake Arewacin Mali, inda ake sa ran nan gaba zai tattauna da Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

Talla

Ziyarar ta Ministan na zuwa ne bayan cika shekara daya da jagorantar yaki da Faransa ta yi domin kakkabe ‘yan tawayen kasar Mali inda ya fara yada da zango a birnin Gao wanda a da yake hanun ‘yan tawayen.

Ana kuma sa ran zai tattauna da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a lokacin wannan ziyara.

Kuma kamar yadda rahotanni ke nunawa, Maksudin zuwa kasar shine tattaunawa akan aikawa da dakaru zuwa yankin kasashen Sahel da kuma batun rikicin siyasar kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Wannan ziyara dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Faransa da na Chadi dake kasar suka wargaza makamai masu tashi da yawansu ya kai tan shida a jiya, wanda ake kallon hakan a wani koma baya ga farfadowar ‘yan tawaye a kasar.

Wannan kuma shine kuma karo na biyu cikin watannin uku da ake lalata irin wadannan makamai, domin ko a watan Satumba dakarun Faransan sun gano wata mota dinke da bama bamai a Arewacin garin Anefis dake Malin.

Ana dai sa ran Minista Le Drian zai wuce zuwa kasashen Jamhuriyar Niger da kuma Chadi a wannan rangadi da yake yi na kwanaki uku.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.