Faransa

Manuel Valls ya zama sabon Firaiminista a Faransa

Manuel Valls, sabon Firaiministan Faransa
Manuel Valls, sabon Firaiministan Faransa REUTERS/Benoit Tessier/Files

Shugaban kasar Fransa Francious Hollande ya nada yardajjensa kuma tsohon Ministan harkokin cikin Gida Manuel Valls a matsayin Firaiministan kasar Fransa, bayan murabus din da Jean Marc Ayrolt da gwamnatinsa suka yi a ran Litanin. Ga dai takaitaccen bayani kan Manuel Valls, ma’ana sabon Firaiminista

Talla

An haifi Manuel Carlos Valls ne, a ranar 13 ga Watan Ogustan 1962 da misalin karfe 8 na Dare a Assibitin La Ferro Viaria da ke kan hanyar Campoamor a unguwar Horta, dake birnin Barcelona na kasar Spain, ya rikide ya zama bafaranshe ne a shekarra 1982, inda ya zama daya daga cikin manyan yan siyasar kasar Fransa.

Vallas ya yi karatun jam’ia inda ya fito da Takardar shaidar kwarare kan karatun tarihi

A baya dai Manuel Valls ya taba rike mukamin magajin garin Evry a shekarar 2001, a sekarar 2012 kuma, ya tsaya takarar neman jam’iyarsa ta socialist ta tsayar da shi takarar dan majalisar dokoki a zaben 2011, kafin ya zama Daraktan yada labarai na Francois Hollande a lokacin yakin neman zaben shugabancin kasar na 2012.

Bayan cin nasarar zaben shugaba Hollande ya nada shi a kan mukamin ministan cikin gidan kasar Faransa, a gwamnatin farko ta Firaiminista Jean Marc Ayrault ta 1, mukamin da ya ci gaba da rikewa har zuwan gwamnati Ayrault ta 2.

Masu iya Magana na cewa, faduwar wani tashin wani, a yayinda jam’iyyar Socialist ta sha kashin da bata taba sha ba a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a ranar lahadin da ta gabata, al’amarin da yayi sanadiyar murabus din Firaiminista Jean Marc da Gwamnatinsa, a ranar Litanin ta 31 ga Wata Maris, shugaba Hollande ya nada, Manuel Valls kan mukamin Premier Ministan kasar ta Faransa inda jan aikin sake farfado da tattalin arziki da kuma kokarin maido da martabar gwamnatin ga idon faransawa ya dogara a kansa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.