Faransa

Sabon Fira Ministan Faransa ya bayyana rage kashe kudade

Sabon Fira Ministan Faransa Manuel Valls yayin da yake jamabi gaba malisa
Sabon Fira Ministan Faransa Manuel Valls yayin da yake jamabi gaba malisa REUTERS/Charles Platiau

Sabon Fira Ministan kasar Faransa Manuel Valls ya bayyana sabbin matakai na kara farfado da tattalin arzikin, a wani jawabin sa na farko gaban majalisar kasa.Manuel Valls wanda Shugaba Francois Hollande ya nada makon jiya, bayan da jamiyyar dake mulki ta Socialist ta sha mamaki a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar yayi alkawarin ganin ya tafi da kowa a cikin wannan tafiya.Ya bayyana matakan da zasu taimakawa ma'aikatu diban ma'akata, domin rage rashin ayyukan yi, inda yace matakan zasu sa a rage kudaden da suka kai kudin Turai Euro biliyan 30.Karkashin yarjejeniyar kungiyar Turai ta kulla da Faransa, kudin da suka kai Euro biliyan 50 ne za’a zabtare daga kasafin kudin kasar, da suka hada da Euro biliyan 10 daga kananan hukumomi, euro biliyan 19 daga Gwamnatin kasa, da euro biliyan 10 daga kasafin kudade na fannin lafiya.PM ya kuma yi amfani da damar wajen yin watsi da zargin da Shugaban Rwanda Paul Kagame yayi na zargin FR da hannu wajen kisan kiyashi.