Obama ya bayyana wa Poutine damuwarsa dangane da rikicin Rasha
Wallafawa ranar:
Duk da tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a jiya litinin, shugaban Amurka Barack Obama da takwaransa na Rasha Vladamir Poutine, sun gaza warware sabannin da ke tsakaninsu dangane da rikicin Ukraine.
Bayanai daga Washington na cewa shugaba Obama, ya bayyana wa takwaransa Poutine matukar damurwarsu dangane da irin rawar da Rasha ke takawa a rikicin na Ukraine, yayin da Poutine ya ce bayanai da ke cewa kasarsa na da hannu a wannan rikici zargi ne maras tushe.
A daya bangare kuwa shugaban hukumar leken asirin Amurka wato CIA ya kai ziyara a asirce a birnin Kiev karshen makon da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu