Ukraine-Rasha

Zaben raba gardama a yankin Donetsk da Lougansk na Ukraine

Rumfar zabe a garin Marioupol a ranar 11 ga watan Mayu 2014.
Rumfar zabe a garin Marioupol a ranar 11 ga watan Mayu 2014. REUTERS/Marko Djurica

Masu goyon bayan kasar Rasha a yankin gabashin Ukraine a yau lahadi sun ki sauraren matsin lambar kasashen duniya inda suka ci gaba da gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a domin ballewa daga Ukraine kana su hade da kasar Rasha.

Talla

Ana dai gudanar da kuri’ar ne a lardunan Donetsk da kuma Lougansk, inda ake da mutane akalla milyan 7 da dubu 500 a cikin mutane milyan 43 da kasar ta Ukraine ta kunsa.

To sai dai masu ra’ayin ci gaba da kasancewa karkashin ikon kasar ta Ukraine sun kaurace wa zaben na yau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI