Faransa

Ziyarar Hollande a wasu kasashen Tsohuwar Daular Soviet

Ziyarar Shugaban Faransa François Hollande a Azerbaijan
Ziyarar Shugaban Faransa François Hollande a Azerbaijan REUTERS/Fuad Esgerov/Pool

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya fara zirarar kwanaki uku a wasu kasashen tsohuwar Daular Soviet da suka hada da Azerbaijan da Armenia da Georgia domin inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen da Turai. Wannan kuma na zuwa ne a yayin da kasashen Turai ke takun saka da Rasha saboda rikicin Ukraine.

Talla

Shugaba Hollande ya fara kai ziyara ne a kasar Azerbaijan a ranar Lahadi kafin ya je Armenia da Georgia, kasashe da ke yankin kudancin Caucasus da ke kan iyaka da Turai da kuma Asiya.

Ziyarar Hollande dai na zuwa ne a yayin da kasashen Turai ke takun saka da Rasha saboda rikicin Ukraine. Kuma a birnin Baku na Azerbaijan Hollande ya yi Allah waddai da zaben ballewa daga Ukraine da mutanen gabacin kasar suka gudanar da ke kishin Rasha.

Hollande ya gana da shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan, da niyyar inganta huldar Turai da kasar, A yau Litinin ne kuma shugaban na Faransa zai mika zuwa Armenia, zuwa gobe kuma ya kai ziyara Georgia.

Amma kamar kasar Ukraine da ke ra’ayin Turai bayan hambarar da Gwamnatin Yanukovich, haka ma kasashen uku sun fi kaunar shiga Tarayyar Turai fiye da Rasha. Kuma akwai yarjejeniyar kasuwanci da Turai ke son kullawa da kasashen na Tsohuwar Daular Soviet, wanda shi ne tushen rikicin kasar Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI