Ana zaben 'yan majalisun kungiyar taraiyyar Turai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yau lahadi ake shirin zaben ‘yan majalisun dokokin kungiyar kasashen nahiyar Turai EU, a kasashen Girka, Romania da Lithwania. Wannan ce ranar karshe a zaben mai cike da muhimmanci, kuma ana ganin jama’iyyun da ke dari dari da shirin hade kasashen Turai zasu sami karin tasiri.Kashen na EU 21 ne zasu yi zaben a yau Lahadi, da suka hada da Faransa, Jamus da Italiya, inda za a kammala zaben na kwanaki 4, da aka fara a Britaniya da Netherlands ranar Alhamis.