Belgium

Mutane 3 sun mutu a wani harin da aka kai wa yahudawa a Brussels

Wani gidan tarihin Yahudawa da ke birnin Jerusalem
Wani gidan tarihin Yahudawa da ke birnin Jerusalem Reuters

A kalla mutane 3 sun mutu, yayinda mutum daya ya sami rauni, sakamakon harin da dan bindiga ya kai a wani gidan tarihin Yahudawa, da ke birnin Brussels na kasar Belgium.2 daga cikin wadanda suka mutu Yahudawa ne, Prime Minista kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu yace harin na nuna yadda ake kyamar Yahudawa a kashern nahiyar Turai.A nashi bangaren, Prime ministan kasar ta Begium Elio Di Rupo, daya kira taron manema labaru na gaggawa, yace duk da hadin kan da ‘yan kasar ke da shi, an kai hari na nuna kiyayya.