China-Amurka

Ana hararan juna tsakanin China da Amurka da Japan kan Tekun Asiya

southeastasiaview.blog...

Kasar China ta mayarwa da kasashen Amurka da Japan martani bisa zargin da suka yi na tayar da hargitsi a kan tekun Asiya da kasashen yankin ke takaddama a kai

Talla

A karshen makon da ya gabata ne Sakataren tsaron kasar Amurka Chuck Hagel ya zargi kasar China da haifar da rikici a yankin Tekun Asiya, inda ya gargadi hukumomin kasar da su kaucewa tada zaune tsaye a yankin.

Sai dai a wasu kalamai da ake ganin na mayar da martani ne, mataimakin babban hafsan sojin kasar China Laftanar Wang Guanzhong, ya zargi Shugaba Shinzo Abe da Hagel da yunkurin shirya kai hari akan China.

A cewar Wang, jawaban da Abe da Wang suka gabatar basa dauke da wani sako illa sakon tunzura kasar China, ya kuma kara da cewa China ba za ta taba amincewa da wata kasa ta nuna mata iko akan kasar ta ba.

China da Japan dai suna takaddama ne kan wasu Tsibirai da ke a gabashin Tekun China, inda bangarorin biyu ke ikrarin nasu ne yayin da kasar Amurka ke nuna fifiko kan kasar Japan a cikin wannan takaddama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.