Faransa

Rayayyun bama-baman da aka yi amfani da su a yankin duniya na biyu

sojoji a yakin duniya na biyu
sojoji a yakin duniya na biyu Göttert/ German Federal Archives/ Wikimedia CC

Robin des Bois, kungiya ce mai zaman kanta a Faransa ta fitar da sakamakon wani bicinke da ke tayar da hankali a game da yadda jama’a ke ci gaba da rayuwa tare dimbin makamai da kuma nakiyoyi da aka yi amfani da su a yankin duniya na biyu.

Talla

Sakamakon dai na nuni da yadda yanzu haka rayayyun bama-bamai da ake jefa kan kasar Faransa lokacin yakin duniya na biyu ke ci gaba da kasancewa warwatse a sassa daban na kasar ba tare da an fashe su ko kuma kwance sub a.

Kungiyar ta ce an fi samun irin wadannan abubuwa masu fashewa ne a yankin kudu maso yammacin kasar, inda sojojin kawance na Amurka, Birtaniya da kuma Canada suka share tsawon lokaci suna ruwan bama-bamai a kan sojoji ‘yan Nazi da ke mamaye da kasar ta Faransa a lokacin yakin duniya na biyu.

Kungiyar ta ce daga shekarar 1940 zuwa 1945, an jefa bama-bamai har guda dubu 600 a Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.