Fransa

An nuna hoton wani Bafaranshe da aka sace a Mali

Hoton Serge Lazarevic da wata tashar Larabawa ta nuna
Hoton Serge Lazarevic da wata tashar Larabawa ta nuna DR

Wani gidan talebijin a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira Al’an, ya watsa hoton bidiyon dan kasar Faransan nan Serge Lazarevic da ake yin garkuwa da shi bayan an sace shi a kasar Mali a shekarar 2011.

Talla

Gidan talabijin din dai ya nuna hoton bidiyon Serge Laza-revic ne sanye da wata bakar riga, ya kuma tara gemu mai tsawo, inda kuma aka nuna wasu mutane dauke da makamai a gefensa.

A cikin Hotan bidiyon, Lazarevic ya yi kira ga shugaban kasarsa wato Francois Hollande da ya taimaka wajen ganin an ceci rayuwarsa.

An dai sace Lazarevic ne dan shekaru 50 a watan nuwambar shekarar 2011 a kasar Mali tare da Philippe Verdon wanda aka kashe tun cikin watan Yulin bara.

Ana dai zargin kungiyar Al Qaeda dake yankin Magrib ne da sace Laza-revic tare kuma da kisan Verdon, yayin da Faransawan ke cikin wani otel dake Arewacin kasar Mali.

Har ila yau ana zargin kungiyar da kisan wasu Faransawa biyu ‘yan jarida da aka kashe a watan Nuwambar bara a kasar ta Mali. Lazarevic dai shi ne bafaranshe kadai da ake garkuwa da shi a duk fadin duniya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI