Jamus-Amurka

Jamus ta kaddamar da bincike akan nadar bayanan Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Barack Obama na Amurka
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Barack Obama na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque

Kasar Jamus ta kaddamar da bincike kan zargin da ake wa kasar Amurka game da satar bayanai na wayar salular Shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel. Babban mai shigar da kara a kasar ta Jamus, Hareld Range ne ya bayyana wa Majalisar dokokin kasar a jiya cewa ya kaddamar da bincike kan kasar Amurka, lamarin da ya gurgunta dangantaka tsakanin kasashen biyu.