Faransa

An soma shagulgulan bukin shekaru 70 na kwatar Faransa daga 'yan Nazin Hitla

Dirar Soji a Normandy
Dirar Soji a Normandy charliedavis.us

Ranar 6 ga Watan Yuni ce ranar bukin tunawa da zagayowar shekaru 70 da kwatar kasar Faransa daga Dakarun Nazin Hitla na kasar Jamus a shekarar 1944. An ce dai bukin zai samu halarcin shugabannin kasase daga sassan Duniya baki daya, kuma tuni shugaban kasar Amurka Barack Obama da Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta 2 da Waziriyar Jamus Angela Markel da shugaban kasar Fransa Fracios Holland sun hallara a Normandy domin wannan buki  

Talla

Yanzu haka an fara hidimomi kan bukin cikar shekaru 70 da jibge Dakarun hadin Guiwa na Duniya domin kwatar kasar Faransa daga mamayar Hitla na Jamus.

Ranar 6 ga Watan Yuni ce ranar da Sojojin kundumbala suka dira a Normady ta kasar Faransa domin soma aikin kwatar kasar daga Hitla a shekarar 1944.

An dai shirya bukukuwa da dama da za’ayi ciki kuwa, hadda karrama wasu Sojin kundumbala na kasashen Duniya da suka yi dauki ba dadin kwatar Faransa daga Dakarun Nazin Hitla.

Akalla dai an kashe fiye da Dakaru 4,500 daga cikin Dakaru 156,000 da aka jibge a yankin Normandy a ranar 6 ga Watan Yunin shekarra 1944.
Yarima Charls na kasra Ingila ma ya jagoranci karrama Mazan fama da suka ja daga a rana ta farko ta fara yakin da ya kai ga kama Sojin kasar Jamus a wani samame mai ban mamaki.

A wani bangare na bukin haka ma Dakarun kasashen Amurka da Faransa da Jamus za su hallara a gabar Ruwan Utah da ke a yankin yammacin gabar Ruwan da wannan mamayar ta auku.

Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta 2 da shugaban kasra Amurka Barak Obama na daga cikin muhimman mutanen da suka halarci wannan kasaitaccen buki.

Rahotanni dai na nuna yanda masu wasa da kayan Wuta ke ci gaba da shiryawa domin cika sararin samaniya da haske a tsakkiyar Daren yau Alhamis wayewar gari gobe Jumu’a da za’a gudanar da bukin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.