Syria-Amurka

Amaruka ta sanar da taimakawa yan tawayen Syria

Shugaban kungiyar  yan Shi’a  yankin kasar Lebanon, Hassan Nasrallah
Shugaban kungiyar yan Shi’a yankin kasar Lebanon, Hassan Nasrallah REUTERS/Khalil Hassan

Shugaban kungiyar yan Shi’a yankin kasar Lebanon, Hassan Nasrallah yayi kira ga yan tawayen Syria da su aje makamai, tare da kawo karshen zubar da jini a kasar.A wata zantawa da ya yi da tashar talabijen ta kungiyar Hezbollah mai goyan bayan Shugaban kasar Syria Bashar al Assad, Hasan Nasrallah ya bayyana fatan ganin an hau teburin sasantawa tsakani Gwamnatin Shugaba Bashar Al Assad da yan tawayen kasar.  

Talla

Wanan kira dai na zuwa ne, yan kwanikin da gudanar da zaben shugabanci kasar a farkon wannan mako, zaben da hukumar zaben ta kasar ta ce, Shugaba Assad ne ya lashe shi, da kusan kashi 88 cikin dari na kuri’un da aka kada .

Ta bakin Susan Rice mai baiwa shugaba Obama shawara kan sha’ani tsaro, kasar Amaruka ta bayyana aniyarta wajen taimakawa yan tawayen Syria da makaman da suka dace su tunkarin dakarun gwamnatin Bashar al Assad da su .

Rice dake cikin tawagar masu rakiyyar Shugaba Obama a kasar Faransa ,ta bayyana matsayin kasar Amaruka wajen ganin an kawo karshen mulkin shugaba Bashar al Assad a cikin kankanin lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.