Serbia

Ana zargin Ministan Serbia da satar Jarabawa

Nebojsa Stefanovic, Ministan Cikin gida da ake zargi ya saci jarabawa
Nebojsa Stefanovic, Ministan Cikin gida da ake zargi ya saci jarabawa novinenovosadske

Majalisar dokokin kasar Serbia zata fara binciken zargin satar fasaha, da ake yi wa sabon ministan harkokin cikin gidan kasar Nebojsa Stefanovic, lokacin da ya ke karatun digirin digirgir. Shugaban Kwamitin da ke bincike kan batun Aleksandra Jerkov yace zasu duba zargin da wasu shehunnan malaman boko suka yi wa Minstan.

Talla

Sai dai ministan mai shekaru 37 da haihuwa, da ya karbi mukamin a watan Afrilu, ya musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.