Ukraine

An rantsar da sabon Shugaban Ukraine Petro Porochenko

Petro Porochenko, zababben shugaban Ukraine
Petro Porochenko, zababben shugaban Ukraine REUTERS/David Mdzinarishvili

A yau asabar ne aka rantsar da Petro Porochenko a matsayin shugaban kasar Ukraine, bayan nasarar da ya sama a zaben da aka gudanar kimanin makonni biyu da suka gabata a kasar.

Talla

Porochenko , wanda ke gabatar da jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi a zauren majalisar dokokin Kiev babban birni kasar ,

Sabon shugaban  Ukraine ya dau alkawalin aiwatar da sabuwar siyasar da za ta kai ga samar da konciar hankali da zaman lafiya mai dorewa a Ukraine duk da yake ya bayyana adawar sa zuwa shugaban Rasha Vladmir Poutine a ganawar da suka yi a Faransa da cewa Ukraine ba zata darewa gida biyu ba.

An dai gudanar da wannan biki ne a gaban dimbi jama’a da suka hada da mataimakin Shugaba Obama Joe Biden, shugabannin kasashen Turai, da dai sauransu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.