Spain

Ana zanga zangar adawa da masarautar kasar Spain

Tshon sarkin kasar Spain Juan Carlos
Tshon sarkin kasar Spain Juan Carlos REUTERS/Sergio Perez

Dubun dubatar ‘yan kasar Spain sun yi zanga zanga a manyan titunan birnin Madrid, inda suke so a yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a, don soke masarautar kasar. Wannan na zuwa ne a kwanakin kadan bayan sarki Juan Carlos ya sauka daga mukaminshi, inda ya baiwa dan shi Felipe.A shekarar 1975 Juan Carlos ya dare gadon sarautar Spain, kuma ana girmama shi saboda ci gaba daya samar, sai dai farin jinin shi ya dusashe bayanda aka sami wasu daga cikin iyalan shi da cin hanci a shekarar 2011, lokacin da kasar ke fuskanatar matsalar tattalin arziki.