Kotu Rasha ta yankewa mutane biyu hukuncin daurin rai da rai kan kisan 'Yar jarida

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin

A yau litinin kotu a kasar Rasha ta zartar hukuncin daurin rai da rai akan wasu mutane biyu bisa samun su da liafin kashe wata ‘yar Jarida mai suna Anna Politkovskaya.

Talla

Kotun ta kuma hukumta wasu uku dake da hannun a kisan inda tayanke musu hukuncin daurin shekaru tsakanin 12 da 20 a gidan yari.

Politkovskaya mai shekaru 48 a duniya ta gamu da ajalin ta ne a hannun mutanen a gidan ta dake birnin Moscow a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2006.

Ita dai Politkovskaya ta kasance tanawa gidan jaridar Liberal ta Novaya Gazeta, wadda kan rubuta labarai dake yawan sukan gwamnatin Rasha.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.