Brazil 2014

Zanga-zanga a Birni Sao paulo

Wasu masu zanga zangar a Sao Paulo dake Brazil
Wasu masu zanga zangar a Sao Paulo dake Brazil REUTERS/Stringer/Brazil

Hukumomi a kasar Brazil sun himmatu ga tabbatar da nasara a gasar cin Kofin kwallon Kafa ta Duniya da za’a fara a jibi Alhamis.Sai dai babbar matsalar da ake fuskanta ita ce yajin aikin da ma’aikatan samar da kayan kwalama na gidajen sayar da abinci ke shirin somawa a ranar da ake shirin buda gasar.

Talla

Wannan dai babbar matasala ce, idan aka lura da yanda hukumomin kasar ke cike da bukatar burge Duniya a yayin gudanar da gasar da a wannan shekarar kasar ta Brazil ce ke daukar bakuncinta.

Kamin wannan batu na yajin aikin ma’aikatan dai, sai da aka samu jerin zanga-zangogi daga kusan kowace kusurwa ta kasar Brazil inda mutane ke nuna bacin ransu da abinda suka kira almubazzarancin da suka ce gwamnatin kasar ta yi na kashe makudan kudade fiye da Dallar Amurka Billiyan 11.

Akasarin al’ummar kasar dai na ganin zai fi dacewa da gwamnatin Brazil ta zuba wadannan kudaden ne a fannin samar da Ilimi, a yayin da hukumomin kasar ke fadar cewar ta yi hakan ne domin kara janyo wasu kudaden ta hanyar ribar da za ta samu bayan kammala gasar.

Sao Paulo na fuskantar babbar matsala kan batun yajin aikin da ma’aikatan a ranar farko ta soma gasar.

Sai dai ma’aikatan sun bayyana janye yajin aikin kwanaki 5 da suka gudanar da kuma ya haddasa tsananin cinkoson ababen hawa

Ba da jimawa ba ne ake sa ran Sakataren Majalisar dunkin Duniya Ban Ki-moon da shugabannin manyan kasashe 12 za su hallara a babban filin wasar da aka ce ma’aikata na can suna hanzarin kamala aikin shi kamin wa’adin soma gasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.