Lafiya

Masana a kasar Birtaniya na kokarin hana Sauro Haihuwar jinsin Mata

en.wikipedia.org

Masana kimiyyar Rayuwa sun bada shawarar yin amfani da wata hikima ta hana Sauro haihuwar ‘ya’ya mata ta hanyar rage masa karfin bada kwayoyin halitta masu samar da ‘ya’ya mata a lokacin saduwa da Matansu

Talla

Masanan sun gabatar da wanan shawarar ne bayan wani bincike da suka gudanar a wata Cibiyar bincike da ake kira Imperial Collage ta birnin London na kasar Burtaniya.

To ko hakan na yiyuwa tambayar kenan da muka yiwa Phamacist Murtala Bello masani fasahar harhada magunguna a jihar Sokoto wanda ya ce babbar hanyar hana Sauro cutawa bil’adama itace ta hanyar hana shi haihuwa.

Sai dai yunkurin da Masala ke yi domin hana Sauron haihuwar ‘ya’ya mata zuwa akalla kashi 5 na iya taimakawa idan haka ta tabbata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.