Amurka

‘Yar wasar Fim a Amurka Agelina Jolie, ta bukaci a hana yiwa Mata Fyade

stuff.co.nz

Angelina Jolie wadda shahararriyar Jarumar Fina-finai ce a kasar Amurka da kuma ta yi fice a fina-finai da dama ta fada a wani babban taron da ake domin tattana batun cin zarafin Mata ta hanyar Fyade a Duniya cewar matsalar babba ce kuma akwai bukatar masu rike da madafun iko da su yi kokarin kawar da ita

Talla

A taron da ake yi a birnin London domin duba lamurran da suka shafi muzgunawa da cin zarafin mata shahararryyar ‘yar Fim din nan ta kasar Amurka Anjelina Jolie ta yi jawabi a gaban taron inda take cewa Ba abin kunya bane mace ta tsira da ranta bayan an yi mata fyade maimakon haka kunya na ga wadanda suka aikata fyaden akan ta.

Jolie ta ce Canfi ne, cewa babu yadda za’a kauracewa fyade lokacin a yaki.

Ta ce sanin kowa ne a fagen daga dai makamai ne da ake anfani da su a lokacin yaki akan fararen hula amman babu wata dangataka da yin jima’i.

Angelina Joliet a bayyana cewar ta hadu da Mata da dama da aka yia Fyade a kasashe kamar Afghanstan da Somalia, kuma ta ce bata ga banbanci tsakaninsu da Matan da ke a Nahiyar Turai ba, illa abu daya.

Banbancin kuwa a ta Bakinta shi ne su suna zaune ne a Kassahen da hakan bata faruwa, kuma akwai Likitocin da ka iya daukar mataki kai tsaye ga Macen da aka lalata.

Su kuma Matan da ta zanta za du na zaune ne a Sansanonin ‘yan gudun Hijira inda, a fili gashi kuma babu Doka da oda, babu kariya ballantana su dubi a yi masu Adaci idan matsalar da ake gurfana a gaban Kuliya ta samu.

Joliet a bukaci a yi wata hubbasa a Duniya domin hana aukuwar ire-iren laifuka na cin zarafin Mata, kuma a daina kyamar Matan da aka yiwa Fydae domin yin hakan ka iya sakasu cikin matsananciyar damuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.