Iran-AIEA

Za’a sake zama da Iran akan shirinta na Nukiliya

IRAN
IRAN

Ana sa ran gungun kasashe Biyar na Turai za su sake zaman tauttaunawa da kasar Iran dangane da batun Nukliyar kasar da ya ki ci ya ki cinyewa. Sanarwa dai ta futo daga Bakin Ministan harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius

Talla

Laurent Fabius ya ce za mu sake zaman Tauttaunawa tsakani Faransa da Teheran a ranar Laraba, kuma mu cima matsaya ta sake yin dubi kan batutuwa da suka shafin kasar ta Farisa wato Iran, da sauran kasashe Biyar da kuma kuma kimanin kungiyoyin kasashe shida.

Bayan haka ne za mu sake dawowa Teburin tauttaunawa da kasar ta Iran.

Batun aikin sarrafa makamashin Uranium da kasar Iran ke yi dai na ci gaba da tada hankalin kassahen yammacin Duniya da Israela mai yiwa Iran kallon babbar matsalar da take fuskanta a yankin kassahen Larabawa.

A baya dai Manyan kassahen Duniya da suka hada da Amurka da Faransa da China da Jamus da Rasha sun sanya Iran a gaba tare da gudanar da zaman Teburin tattaunawa a Geneva inda aka fito da wata yarjejeniyar da Iran ta mutunta, sai dai daga baya anyita fito da rade-radin cewar kasashen sun dan kaucewa biyan bukatun kasra Iran abinda ya kai Iran ga kalubalantar kasashen da ta kira masu dora mata Kahon zuka.

Iran dai ta tsaya akan cewar aikin sarrafa makamashin Uranium da take na biyan bkatun al’ummarta ne ba samar da Makamai ba.

Amma duk da hakan kasar Israela da ta zargi Amurka da yiwa al’amarin Iran rikon Sakainiyar Kashi a baya bata samu natswa da aikin Uranium din kasar Iran ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.