Birtaniya

Ana taron yaki da cin zarafin mata a lokacin yaki

Angelina Jolie tare da ministan harkokin wajen Britaniya William Hegue
Angelina Jolie tare da ministan harkokin wajen Britaniya William Hegue reuters

An shiga rana ta 3 an zaman taron kawar da yi wa mata faide a lokutan yaki, a karakashin jagorancin shaharariyar ‘yar wasan fim din nan ta kasar Amruka Angelina Jolie, da ministan harakokin wajen kasar Britaniya William Hague. Ana dai gudanar da taron ne a birnin Landon na kasar Britaniya.Sai dai kuma daura da zaman taron na yau ministocin harakokin wajen kasashen duniya sun buda wani zaman taro kan matsalar tsaron a yankin arewacin tarayyar Nigeria, inda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da yin garkuwa da mata sama da 200Garkuwar da kungiyar mayakan Boko Haram ta yi da dalibai yan mata sama da 200 a garin Chibok dake jahar Borno ne, ya ja hankalin mahalarta wannan taron da ake yi, don kawar da cin zarafin mata a yankunan da ake fama da yake yake a duniya inda ake yiwa mata Fyadeministocin harakokin wajen da ke halartar taron na birnin Landon, a yau alhamis sun kebe kansu daura da zaman taron, inda suke tattaunawa kan matsalar da kungiyar Boko Haram ke haifarwa a taraiyyar Nigeriaministocin zasu duba hanyoyin da ya dace a bi wajen kawo karshen ayyukan kungiyar, da kuma barazanar da take haifarwa al’umma, ba ma a Najeriya ba har da sauaran kasashen makwabta, da ke yankin yammaci da tsakkiyar nahiyar Afrika. zaman taron ya zone bayan gudanar da wani zaman taro makamancinsa da a aka gudanar a ranar 17 ga watan mayun da ya gabata a birnin Paris na kasar Fransa, kan matsalar kungiyar ta Boko Haram, da Amruka da sauran kasashen yammaci suka saka a cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda, dake barazana ga zaman lafiyar duniyayanzu haka dai kungiyar Boko Haram da Abubakar Shikau ke jagoranta, ta kara rubanya hare haren da take kaiwa a yankunan arewacin Nigeria, tun bayan garkuwar da ta yi da ‘yan matan na garin Chibok a jahar Borno su sama da 200, watanni 2 da suka gabata.Tuni shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shikau yace zai sayar ya kuma aurar dasu ga mayakansa, har yanzu kuma babu duriya ko labarin inda yaran suke.