Spain

Majalisar Spain ta amince da murabus din Sarki Carlos

Sarkin kasar Spain mai murabus, Juan Carlos
Sarkin kasar Spain mai murabus, Juan Carlos REUTERS/Sergio Perez

Majalisar Kasar Spain ta amince da gagarumin rinjaye dangane da bukatar Sarki Juan Carlos na sauka daga karagar Sarautar kasar, duk da adawar da aka samu na yin hakan, matakin da zai bude hanyar bai wa Dan sa Felipe damar maye gurbinsa. ‘Yan Majalisu 299 suka goyin bayan bukatar, yayin da 19 suka ki amincewa, 23 suka ki kada kuri’a.

Talla

A ranar 17 ga wata ne Majalisar Dattawan kasar za ta kada kuri’ar amincewa da matakin.

A ranar 2 ga watan Yuni ne juan Carlos ya bayyana ya kawo karshen mulkinsa bayan shafe shekaru 39 yana Sarki a Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.