Spain

Felipe sabon Sarkin Spain

Sarki Felipe na Spain tare da sarauniyarsa Letizia
Sarki Felipe na Spain tare da sarauniyarsa Letizia REUTERS/Juan Medina

Sarkin Juan Carlos na Spain ya mika ragamar mulki ga dansa Felipe wanda aka rantsar a yau Alhamis a zauren Majalisar kasar. Wannan ne karon farko da aka samu sauyin Sarki a masarautar Spain tun da kasar ta dawo mulkin demokuradiya.

Talla

Sarki Felipe ya gabatar da jawabi a gaban Majalisa bayan an rantsar da shi inda ya dauki alkawalin  yin aiki da kundin tsarin mulki.

Kafin Sarki Carlos ya mika mulki ga dansa sai da dukkanin bangarorin siyasar kasar suka amince da matakin bayan ya yi murabus.

Juan Carlos mai shekaru 76 cikin hawaye ya sanya hannu ga takardar murabus a gidan Sarautar Spain.

Sarki Carlos ya yi gwagwarmayar tabbatar da mulkin demokuradiya a Spain bayan mutuwar Janar Francisco Franco, sai dai kuma akwai binciken badakalar haraji da ake wa ‘Yarsa Gimbiya Cristina wanda wannan kalubale ne ga sabon Sarki Felipe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.