Iran-Iraq

Pentagon - Iran ta aika masana tsaro ‘yan kadan a kasar Iraqi

dubaiforums.com

Hukumar tsaro ta kasar Amurka ta bayyana cewar sabbin bayannai da ke fitowa daga kasar Iraqi na nuna cewar kasar Iran ta aike da kalilan daga cikin kwararrunta masana harkokin tsaro a kasar Iraqi

Talla

Hukumar tsaron ta kasar Amurka wato Pentagon ta ce Iran ta aika kwararrun ne domin su taimakawa gwamnatin Firaiminista Nuri al-Maliki da wasu hikimomin da zata iya magance tada kayar bayan da ke faruwa a kasar, bayan wasu kazammun hare-haren da aka kai da suka hallaka Jami’an tsaro 34.

Sai dai Pentagon bata bayyana matakin na iran a matsayin aika wata Rundunar Sojin kasar zuwa Iraqi ba.

Mai magana da Yawun hukumar saron ta kasar Amurka ya ce ya ga wasu daga cikin jami’an tsaron kasar Iran a Iraqi, sai dai bai ga alamun sun zu da shirin zama ko gudanar da wani aiki ba ne, kuma bashi da tabbas akan ko iran na shirin jibge Dakarunta na Kudus a Iraqi ko kuma a’a amma dai akwai jami’an Iran a Iraqi.

Iran dai a baya-bayan nan ta yi kakkausar suka ga kasar Amurka kan yanda ta kasa magance matsalar tashin hankalin kasar Iraqin duk da shekaru da Dakarunta suka kwashe suna abinda iran ta kira zaman dirshan a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.