Ukraine

Ukraine: 'Yan a ware sun ki tsagaita wuta

'Yan a ware masu kishin Rasha da ke yaki a Ukraine
'Yan a ware masu kishin Rasha da ke yaki a Ukraine REUTERS/Shamil Zhumatov

A kasar Ukraine an yi musayar wuta tsakanin dakarun gwamnatin kasar da kuma ‘Yan tawaye masu kishin Rasha a gabacin kasar duk da gwamnatin Ukraine ta bayyana matakin tsagaita wuta. Yanzu haka kuma hankalin Ukraine ya tashi bayan da rahotanni suka ce Rasha ta jibge dakarunta a akan iyaka don shirin ko ta kwana.

Talla

Akwai takunkumi da kasar Amurka ta kakabawa shugabannin ‘Yan tawayen maso gwagwarmayar ballewa daga Ukraine tare da yin gargadi ga Rasha akan ta kaucewa aikawa da dakarunta na Soji zuwa Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.