Faransa-Jamus

Hollande da Merkel sun lallashi Putin akan Ukraine

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande yana zantawa ta wayar Tarho
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande yana zantawa ta wayar Tarho elysee.fr

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun yi kira ga shugaban Rasha Vladimir Putin a yau Lahadi da ya nuna goyon bayansa ga zaman sulhu tsakanin gwamnatin Ukraine da ‘Yan tawaye da suka mamaye gabacin kasar.

Talla

Shugabannin na Faransa da Jamus sun zanta ta wayar tarho ne tare da zantawa da Putin na Rasha akan ya taimakawa bangarorin da ke rikici a Ukraine su koma teburin sulhu.

A jiya Assabar dai an yi musayar wuta takanin dakarun gwamnatin Ukraine da ‘Yan tawaye, duk da shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya bayar da sanarwar tsagaita a ranar Juma’a.

A yau Lahadi kuma shugaba Putin ya yi kira ga Ukraine ta tsagaita wuta don bude kofar hawa teburin sulhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.