UNESCO

UNESCO ta karrama wani Kogo a Faransa

Kogon Grotte Chauvet da UNESCO ta karrama mai kunshe da zane kimanin 1000.
Kogon Grotte Chauvet da UNESCO ta karrama mai kunshe da zane kimanin 1000. Wikiemdia Commons / Thomas T.

Hukumar kula da ilimi da al’adu ta UNESCO ta karrama wani kogo a yankin kudancin Faransa mai dauke da zane da wasu abubuwa da ake ganin sune tushen al’adun mutanen Turai. A birnin Doha ne na kasar Qatar hukumar UNESCO ta karrama kogon da ake kira Grotte Chauvet da ke a yankin Ardeche a kudancin Faransa

Talla

Kogon yana kunshe ne da zane sama da 1,000 da aka bayyana sun shafe tsawon shekaru kimanin dubu talatin da shida. Yanzu haka kuma kogon ya kasance wani gidan tarihi ne ga mutanen Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.