Ukraine-Rasha

An fara samun daidaito tsakanin kasashen Rasha da Ukraine

Reuters/Kevin Lamarque

Shugabanin kasashen Rusha da Ukraine sun yi kira ga tattaunawar samar da zaman lafiya a tsakaninsu. Hakan dai ta fara fitowa ne a jiya lahadi a wani mataki na kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a kasar Ukraine

Talla

Wannan matakin na zuwa ne, a daidai lokacin da yunkurin da ake yi, na samar da zaman lafiya a kasar ke cikin halin rashin tabbas.

kiran da shugabanin biyu suka yi dai na zuwa ne bayan kwashe tsawon watanni ana zanga zangar nuna kin jinin yunkurin hada kai da kasashen Turai al’amarin da ya kai ga rasa rayukan jama’a da dama.

Yanzu haka dai shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko ya ce ya zama wajibi su tabbatar da kai karshen rikicin, kuma yin hakan shine wannan matakin na farko da zasu dauka na fara tattaunawa a tasakaninsu.

A dayan bangaren kuma, shugaba Vladimir Putin na kasar Russia ya yi alkawarin amincewa da matakan zaman lafiya da shugaba Poroshenko ke fitowa da su.

Sai dai kuma masu sharhi kan al’amurra na ganin wannan mataki na shugaba Putin a matsayin wata dabara ce ta samun sassaucin takunkuman da kasashen Turai ke kakabawa kasarsa.

A watan Mayu da ya gabata ne dai ‘Yan awaren suka ayyana samun ‘yancin cin gashin kai a yankin Lugansk domin ballewa daga ikon kasar Ukraine abinda ya kai kasar fadawa rikicin siyasar da ya yi sanadiyyar korar shugaba Viktor Yanukovych daga karagar mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.