Ukraine-Rasha

Majalisar dokokin Rasha ta soke damar mamaye Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin

Majalisar dokokin kasar Rasha ta amince da soke zabin da ta dauka na baiwa shugaba Vladimir Putin, damar aikawa da dakarun kasar zuwa Ukraine domin shawo kan rikicin kasar.

Talla

Akalla an samu dan majalisa daya da ya ki amincewa da bukatar da Putin ya aike jiya talata, ta neman a soke damar, wacce aka amince da ita tun a faron watan Maris.

A daya bangaren ‘yan majalisu 153 suka amince da bukatar.

Tuni dai sabon shugaban Ukraine mai samun goyon bayan kasashen yammaci, Petro Poroshenko ya yaba da wannan mataki da Putin ya dauka.

Sai dai duk da haka, Putin ya ce Rasha ba za ta zira ido tana kallo ana muzgunawa ‘yan asalin kasarta dake zaune a gabashin Ukraine ba.

Putin har ila yau ya soki wa’adin da aka shata na tsagaita wuta, inda ya ce mako daya ya yi kadan.

Wannan kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da rahotanni ke nuna cewa magoya bayan Rasha sun kakkabo wani jirgin sojin kasar Ukraine, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji tara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.