EU-Ukraine

EU ta kulla yarjejeniya da kasashen Soviet

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso da Herman Van Rompuy tare da Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko a Brussels
Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso da Herman Van Rompuy tare da Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko a Brussels REUTERS/Stringer

Kungiyar Tarayyar Turai a yau Juma’a ta sanya hannu akan yarjejeniyar hulda tsakaninta da Ukraine da Georgia da Maldova kasashe uku daga tsohuwar daular Soviet domin ci gaba da bijirewa kasar Rasha.

Talla

Kasashen uku sun yi imanin zasu samu makoma mai kyau idan suka kulla yarjejeniya da Tarayyar Turai.

Shugabannin kasashen uku sun sanya hannu kan yarjejeniyar tare da babban Jami’in Majalisar Turai Herman Van Rompuy. Yarjejeniyar ta shafi cinikiyayya tare da bude wa kasashen uku kofar samun wakilci a Tarayyar Turai.

Sanya hannu kan yarjejeniyar wani mataki ne da Ukraine ke fatar kasashen Turai zasu taimaka a kawo karshen rikicin ‘Yan tawaye da suka mamaye gabacin kasar da ke ra’ayin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.