Tarayyar Turai

An zabi Juncker a matsayin shugaban hukumar Tarayyar Turai

Sabon Shugaban hukumar taraiyyar Turai, Jean-Claude Juncker
Sabon Shugaban hukumar taraiyyar Turai, Jean-Claude Juncker REUTERS/Francois Lenoir

Shugabannin kasashen Tirai sun zabi tsohon Prime Ministan kasar Luxembourg Jean-Claude Juncker, a matsayin sabon shugaban hukumar taraiyyar Turai da gagarumin rinjaye. Wannan matakin na matsayin babban koma baya ga Prime Ministan Kasar Britaniya David Cameron da yayi ta kokarin ganin Juncker bai dare mukamin ba, da shine yafi kowanne girma a kungiyar ta tariyyar Turai.Dukkan kasshen na Turai, in banda Shugabannin Britaniya da Hungary, sun kada kuria’ar amincewa da Juncker a matsayin sabon shugaban.Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel, ya bayyana sabon shugaban a matsayin wanda ya kware, da kuma tace zai saurari bukatun kasahen kungiyar da ma majalisar dokokin taraiyyar Turai.Masu lura da lamura suna ganin zaben na juncker zai iya sanadiyyar kasar ta Britaniya ta fice daga kungiyar ta tariyyar Turai.