Rasha-EU-Ukraine

Shugaban Ukraine zai tattauna da Faransa da Jamus kan batun kasar Rasha

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko
Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko Reurters/ Gleb Garanich

Sabon shugaban kasar Ukraine na neman hadin kan shugabannin kasashen Faransa da Jamus, don ganin an shawo kan shugaban Rasha Vladimir Putin, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen 2 ke gab da kawo karshe. Ana sa rai shugaban na Ukraine Petro Poroshenko ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Faransa Francois Hollande, da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, inda dukkansu zasu gana da shugaban na Rasha.Ana sa rai shugabannin zasu yi amfani da tattaunawar ta yau Lahadi wajen shawo kan hukumomin na Rasha, kafin kungiyar taraiyyar Turai da Amurka su kakaba wa kasar takunmi masu tsauri.