Faransa-India

Tawagar manyan jami'an Faransa na ziyara a kasar India

Laurent Fabius, ministan harkokin wajen Faransa
Laurent Fabius, ministan harkokin wajen Faransa REUTERS/Louafi Larbi

Faransa ta kasance kasa ta farko a cikin kasashen Yamma da ta shiga tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da dai sauran bangaroru na alaka tsakaninta da kasar India.

Talla

A yau litinin ne dai ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya isa a birnin New Delhi tare da wata gagarumar tawaga da ta kunshi ‘yan kasuwa da kuma ‘yan siyasa domin tattaunawa da takwarorinsu na kasar India kan batutuwa da dama.

A lokacin da aka zabe shi cikin watan jiya, sabon Firaministan India Narendra Modi ya yi alkawalin aiwatar da manyan sauye-sauye na tattalin arziki da kuma siyasa domin kara kyautata alakar kasar da sauran kasashen duniya.

An dai jima ana tattaunawa tsakanin kasashen biyu a game da shirin sayen wasu jiragen yaki kirar Rafale har guda 126 da India ke kokarin yi daga Faransa, jiragen da kudinsu zai kai dala milyan dubu 12.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.