Tarayyar Turai

Turai na ci gaba da fama da matsalar tattalin arziki

Gini cibiyar Tarayyar Turai a Bruxelles
Gini cibiyar Tarayyar Turai a Bruxelles rnw.nl

Wasu alkalumman ci gaban tattalin arziki na nuni da cewa tattalin arzikin Turai na tafiyar hawainiya, yayin da masana suka bayyana fargaba kan yadda tattalin arzikin Faransa ke ci gaba da tabarbarewa.

Talla

Haka zalika alkalumman sun ce hatta kasar Jamus da ke kan gaba a bunkasar tattalin arziki, a wannan karo tana tafiyar hawainiya ne inda aka kwatanta da yadda yake a can baya, lamarin da ke cusa shakku ga makomar tattalin arzikin Turai.
Kasashen Turai dai da dama ne suka fuskanci matsaloli musamman Portugal, Ireland da kuma Girka wadanda a yau ke fama da dimbin bashin da suka karba karkashin wani shiri na talfawa.
Matsalar dai kamar yadda alkalumman binciken suka nuna, Turai ta fi samun koma bayan tattalin arziki ne daga watan Mayu zuwa watan Yunin bana, yayin da kuma ake ci gaba da samun matsala a lokacin da ya dace ace ana samun ci gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.