Ukraine

An nada sabon Ministan tsaro a Ukraine

Daruruwan masu zanga-zanga a kasar Ukraine
Daruruwan masu zanga-zanga a kasar Ukraine REUTERS/Konstantin Grishin

An nada sabon ministan tsaro a kasar Ukraine, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta bai wa dakarunta umurnin yin amfani da karfi domin murkushe ‘yan aware da suka mamaye wasu birane da ke gabashin kasar.

Talla

Wanda aka nadan mai suna Valeri Gueletei, tsohon jami’in ‘Yan sanda ne, kuma ya yi alkawalin kawo karshe masu tayar da kayar baya.

A yammacin jiya shugaban Amurka Barack Obama da kuma waziyar kasar Jamus Angela Merkel, sun zanta ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladamir Putin, inda suka bukace shi da ya lallashi ‘yan aware domin su ajiye makamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.