Ukraine-Rasha

Dakarun Ukraine sun sami nasara a kan 'yan tawaye masu goyon bayan Rasha

Dakarun Ukraine, da tankar yakin da suka karbe daga hannun 'yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha
Dakarun Ukraine, da tankar yakin da suka karbe daga hannun 'yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha REUTERS/Maria Tsvetkova

Dakarun gwamnatin Ukraine sun sanya Tutar kasar a Birnin Slavyansk, da ke hannun ‘yan tawayen masu goyon bayan kasar Rasha. Dakarun sun sami nasarar sanya tutar ne bayan da suka yiwa akasarin yankuna birnin luguden wuta, lamarin da ake gani a matsayin gagarunar nasara a yakin da hukumomin birnin Kiev ke yi.Mutumin da ya ayyana kanshi a matsayin magajin garin birnin, ya tabbatar da cewa ‘yan tawayen sun fice daga garin da keda yawan mutanen da suka kai dubu 120.