Jamus-Amurka

Kasar Jamus ta kori jami’in leken Asirin Amurka daga kasar

lemonde.fr

Kasar Jamus ta yiwa wani babban jami’in harkokin leken Asiri na kasar Amurka korar Kare daga kasar, a cigaba da sabani da ake samu a tsakanin kasashen Biyu saboda zargin Amurka da leken Asirin kasar ta Jamus 

Talla

Yanzu haka dai kasashen Amurka da Jamus na cikin wani sabani da ake ganin ba’a taba ganin irinsa ba a tsakaninsu, kuma wannan na zuwa ne bayan da Jamus ta gano wasu Amurkawa Biyu masu aikin leken Asirin ta.

Dama dai akwai batun tsohon ma’aikacin leken Asirin Amurkan nan Edward Snowden da ke samun mafaka a kasar Rasha, wanda ya yi ta tone-tonen Sirrin Amurka game da leken Sirrin da take yiwa kasashen duniya.

Gwamnatin Jamus ta fadawa wani jami’in Diflomasiyya na Amurka da ke ofishin jakadancin Amurka a Jamus din cewa ya gaggauta barin kasar.

Steffen Seibert mai magana da yawun Gwamnatin Jamus ya fadi cewa daukar wannan matakin ya biyo ne bayan bincike Biyu da aka gudanar da ke nuna Amurka na ayyukan leken Asiri a Jamus.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai Amurka bata fito fili da wasu bayannai gameda lamarin ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.