Ukraine

‘Yan tawaye sun kashe Sojojin Ukraine

Wani Sojan 'Yan tawaye ya tsaya a kusar da wani wuri da jirgin Sojin ukraine ya fadi
Wani Sojan 'Yan tawaye ya tsaya a kusar da wani wuri da jirgin Sojin ukraine ya fadi (©Reuters)

Rundunar Sojin Ukraine ta tabbatar da mutuwar Sojojinta kimanin 23 sakamakon wata musayar wuta da aka yi tsakaninsu da ‘Yan tawaye da suka mamaye gabacin kasar. Sojojin kasar Ukraine guda 19 ne suka mutu a wasu hare haren rokoki da aka kai a lardin Luhansk, kuma Jami’an tsaron kasar sun zargi ‘Yan tawayen kasar da ke neman ballewa daga Ukraine.

Talla

Rahotanni daga Ukraine din sun ce ‘Yan tawayen sun yi amfani ne da wasu rokoki wadanda Ukraine da Amurka ke zargin sun same su ne daga hannun Rasha.

Akwai wasu Sojojin Ukraine guda 93 da aka ruwaito sun jikkata sakamakon hare haren.

Yanzu haka kuma Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sha alwashin zai mayar da martani, yana mai cewa jinin Soja guda tamkar jinin ‘Yan tawaye 10 ne.

Rundunar Sojin Ukraine tace ‘Yan tawayen sun harbo rokokin ne daga wani kauye da ke kusa da kan iyaka da Rasha. Wannan kuma baraka ce ga kokarin da kasashen Turai da Amurka ke yi na ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.