Ukraine

Jiragen Yakin Ukraine sun yi wa ‘Yan tawaye ruwan wuta

Sojojin Ukraine da suka kwace Slaviansk daga hannun 'Yan tawaye
Sojojin Ukraine da suka kwace Slaviansk daga hannun 'Yan tawaye REUTERS/Gleb Garanich

Gwamnatin Ukraine tace Jiragen yakinta sun yi wa ‘Yan tawaye ruwan wuta a yau Assabar, a gabacin kasar da suka mamaye, bayan Shugaba Poroshenko ya sha alwashin mayar da martani akan hare haren da ‘Yan tawayen suka kai wa Sojojin kasar.

Talla

Kakakin rundunar Sojin Ukraine yace Jiragen yakin sun yi wa ‘Yan tawayen ruwan wuta ne a wani kauye da ke kan iyaka da Rasha.

Jiragen kuma sun yi luguden wuta a Donetsk tare da tarwatsa sansanin ‘Yan tawayen da ke kusa Andriy Lysenko.

A ranar Juma’a ne ‘Yan tawayen suka harbo rokoki tare da kashe Sojojin Ukraine guda 23.

Rundunar Sojin Ukraine ta kiyasta cewa kimanin ‘Yan tawaye 500 ne suka mutu a hare haren da aka kai masu ta jiragen sama a yau Assabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.